- Abba Kyari ya musanta zargin mallakar kadarori
Daga Walid Y Hari
Lauyoyin dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari sun musanta zargin da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta yi na cewa ya ki bayyanna wasu manyan kadarorin da ya mallaka.
A wata sanarwa da lauyansa Barista Hamza Dan tani ya san ya wa hannu ya ce ”An ja hankalinmu kan wani labari da wasu jaridun kasar suka wallafa ranar Litinin inda suke cewa gwamnati ta gano wasu manyan kadarorin Abba Kyari 14 da suka hadar da manyan kantunan sayayya, da filin wasan polo, da gidaje da gonaki”
A cikin Sanarwar lauyan ya musanta wannan ikirari, yana mai cewa sun fahimci hukumar NDLEA na son bata wa Abba Kyari sune ne ta kowane hali, saboda a cewarsa har yanzu mutanen Najeriya na goyon bayan tsohon jami’in dan sandan.