Mayaƙan Boko Haram ‘sama da 100’ sun nutse a cikin ruwa.
Daga Walid Y Hari
Gwamman mayaƙa masu iƙirarin jihadi na Ƙungiyar Boko Haram sun nutse a ruwa yayin da suke guduwa sakamakon luguden wuta ta sama da ƙasa da sojojin Najeriya ke yi musu a a jihar Borno.
Jami’an tsaron Najeriya sun ce sun kai hari ne a maɓoyar mayaƙan a can cikin dajin Sambisa.
Mayaƙan sa kai sun bayyana cewa sun zaƙulo gawarwaki sama da 100 na ƴan Boko Haram ɗin daga cikin kogi inda suka binne su.
Haka kuma ana samun wasu daga cikin mayaƙan na Boko Haram da suke tuba suna miƙa wuta.
Kazalika wasu kuma sun bazama inda suke haɗewa da wasu ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadin irin su ISWAP da ta fi ƙarfi a arewa maso gabas da kuma ANSARU da ke da ƙarfi a arewa maso takiya da kuma wani fanni na arewa maso yammacin Najeriya.