A shirye nake na kwato yankunan da Russia ta mamaye : shugaban Ukraine

Shugaba Volodymyr Zelensky ya sha alwashin kwato dukkanin yankunan Ukraine da Rasha ke ikirarin mayarwa karkashinta, yayinda ya bayyana cewa bazai sake tattaunawa da wani jami’in gwamnatin Moscow ba matukar Vladimir Putin na kan kujerar mulkin kasar.

A jawabin da ya gabatar ga al’ummar kasar bayan Putin ya sanya hannu kan mayar da yankunan 4 karkashin Rasha, Zelensky ya ce zai tattauna da Rasha kan batutuwa da dama amma tare da sabon shugaba ba Putin ba.

Zelensky ya bukaci kungiyar tsaro ta NATO ta shiga rikicin gadan-gadan tare da bai wa kasar damar zama mambarta don kange ta daga makamanciyar mamayar ta Rasha.

Tuni dai shugabannin yankunan 4 da suka kunshi Lugansk da Donetsk da Kherson da kuma Zaporizhzhia suka yi mubaya’a ga shugaba Putin yayin bikin sanya hannu a dokar da ta mayar da yankunan karkashin Rasha jiya juma’a, inda aka hango yadda Putin ke musabaha da shugabannin, irin sa na farko da ya yi mu’amalar fata da fata da wasu mutane tun bayan annobar covid-19.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments