Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da wakilai da ‘yan’uwan mutanen da ‘yan ta’adda su ka yi garkuwa da su bayan sun fasa jirgin kasan da ke jigalarsu daga Abuja zuwa Kaduna watanni sama da hu’du da suka shige.
Wannan ne karon farko da Shugaba Buhari ya gana da dangin fasinjojin bayan da su ka shafe watanni suna jan hankalin gwamnati da ya hada da tattaki zuwa birnin tarayya Abuja inda suka rika gudanar da zangar zangar lumana da kuma zaman dirshe.
A yayin ganawarsa da dangin fasinjojin, Shugaba Buhari ya bayyana dalilan gwamnati na kin amfani da karfin soja domin kwato fasinjojin. Bisa ga cewarsa akwai yiyuwar asarar rayukan wadansu fasinjojin idan aka dauki matakin soja. Shugaban kasar ya bayyana cewa, akwai hatsari sosai wajen amfani da karfin soji idan ba ana da cikken tabbacin ratar da ke tsakanin maharan da wadanda su ke garkuwa da su ba.
Sai dai ya yi alkawarin yin dukan abinda aka iya wajen ceto sauran mutane 31 da har yanzu su ke hannun ‘yan ta’addan. Ya kuma yi alkawarin cewa, nan ba da dadewa ba za a sada su da danginsu.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa, an dauki matakai dabam dabam nan da nan bayan garkuwa da fasinjojin da nufin kwantar da hankalin dangin da kuma ganin hakan ba ta sake aukuwa ba a kasar.
A bayaninsa shugaba Buhari yace, “Na sani cewa, a lokaci irin wannan hankali ya kan tashi,An ba mu shawarwari da dama game da amfani da karfin soji wajen kwato su. An yi nazarin wadannan shawarwari, sai dai an lura cewa, babu tabbacin za a iya ceto su ba tare da asarar rayukan wadansu daga cikinsu ba, dalili ke nan aka yi watsi da wannan shawarar, an ki ana so.”