- Yan uwan wani mutum da ake zargin an kashe shi a jihar Jigawa sun dau alwashin daukar fansa bayan yansanda sun sako wanda ake zargi da laifin aikata kisa
- Shugaban Miyyeti Allah ya ce yansanda sun kira shi dan sanar dashi cewa sun sako wanda ake zargi da kisa kai amma suna cigaba da gudanar da bincike
- Hukumar Yansanda sun ce mutumin da suka sako bashi da alhakin kisan kai da ake zargi yayi a jihar
A Jihar Jigawa Yan uwan wani mutum da ake zargin an kashe shi a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa a ranar Larabar da ta gabata, sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da sakin wanda ake zargin yayi kisan da ‘yan sanda suka yi.
Wanda aka kashe, Yusuf Umar, ya rasu ne a ranar 21 ga Yuli, 2022 a Asibitin Aminu kano dake birnin Kano, kwanaki 18 bayan an kai masa hari a kasuwar karkarar Amaguwa da ke yankin karamar hukumar Ringim.