Hukumar NDIC ta karyata rahotannin da ke cewa an cefanar da POLARIS BANK
Shugaban Hukumar Bello Hassan shine ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wajan taron wayar da Kai ga hukumomin tsaro da Hukumar NDIC ta shirya.
Hassan ya kara da cewa hukumar ta NDIC ta saba gudanar da bincike ga daumacin bankuna domin tabbatar da karfin jarin kowanna banki.