Zargin juyin mulki DSS ta gargadi wasu yan siyasa

Hukumar tsaron farin kaya ta kasa DSS ta gargadi ‘yan siyasa da su kauce wa yin kalamai marasa tushe yayin da ake kusantar zaben shugaban kasa

Gardadin na zuwa ne bayan da daraktan yakin neman zabe na jam’iyyar APC ya zargi sojoji da dan takarar shugaban kasa na PDP da yunkurin yin juyin mulki.

Hukumar ta ce ya zama wajibi jam’iyyun siyasa da masu kula da kafofin yada labaransu su kaurace wa yada labaran kanzon kurege a lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin isar da sakonsu ga magoya bayansu.

Hukumar ta DSS ta ce irin wadannan bayanan marasa tushe bare Makama na iya janyo martani mai zafi daga bangaren hamayya kuma zai iya tada zaune tsaye.

Gargadin na zuwa ne biyo bayan binciken da hukumar ta yi a kan Kalaman Femi Fani-Kayode da ya yi a shafin sa na Twitter wanda ya yi zargin cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar da jami’an tsaro na shirin yin juyin mulki.

A kan hakan hukumar ta yi wa Fani-Kayode tambayoyi ranar Laraba, sai dai hukumar ta DSS ba ta bayyana abin da ta samu tare kayoden ba game da binciken.

A cewar DSS yanzu haka ana fuskantar karuwar yaduwar labaran karya gabanin babban zaben da za a yi ranar 25 ga watan Fabrairu, lokacin da kasar za ta kada kuri’a domin zaben sabon shugaban kasa, inda ‘yan takara uku ke kan gaba.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments