Zan samar da ayyukan da ba ruwan su da shedar Digiri a kasar Amurka—Joe Biden

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana shirin gwamnatin Sa na samar da ayyukan yi ga dinbin matasa da sauran al’umma a kasar ta Amurka.

Biden ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter a yau Alhamis.

Yace aikin da gwamnatin sa zata samar zata samar da shine bisa kokarin sa na rage masu zaman kashe wando a fadin kasar.

Ya kara da cewa aikin zai kasance mai fa’idodin musamman ga matasa da du wanda ya same shi domin za’a sami kyakkyawan biya a cikin sa kuma aiki ne da baya bukatar zurfi karatu ko digiri

Cikin lafazin sa yace “Ina sake gina tattalin arziki da kyawawan ayyuka masu kyakkyawan biya, da basa bukatar shekaru hudu na digiri”

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments