Yan takarar shugaban Kasa a Najeriya sun fara fitar da Manufofinsu da alkawuran da suka daukarwa Yan kasa da zasu Sanya a gaba bayan nasarar zabensu a shekarar 2023.
Wannan ba Sabon Abu bane a duk lokacin zabe idan yazo a Najeriya.
Wasu na ganin kamata yayi Yan siyasa su chanja salon Neman Kuri’un mutane lokacin yakin Neman zabe maimakon yin alkawuran da ba lalle su iya cikawa ba idan an zabesu .
Ku a ganinku akwai hanyoyin da ya kamata Yan siyasa su chanja salon yin alkawarin da ba lalle su cika ba ,ko kuwa suyi shuru da bakinsu yafi zama Alkairi har sai sunyi nasara tukunna?
Muna dakon ra’ayoyinku takan shafukanmu na Aksammedia.