Wani jirgin sama mai zaman kansa da ya ɗauko mutum 5 yan kasar Jamus ya ɓata a sararin samaniya bayan taso wa daga Mexico
Ma’aikatar tsaro ta ƙasar Costa Rica, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace Jirgin ya nufi gabashin ƙasar ne kafin ya ɓata
Ministan tsaron kasar, Jorge Torres, yace zasu yi duk me yuwuwa don gano inda Jirgin ya yi
Jaridar sashin Hausa na Daily Trust tace Jirgin wanda ya ɗauko fasinjoji biyar yan ƙasar Jamus ya bata ne da misalin karfe 12:00 na tsakar dare a Agogon GMT.