Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi wa Festus Keyamo ta-tas kan wasu zargi da ya yi wa gwamnatin GEJ da suka shafi tattalin arziki da danyen man fetur.
Omokri, ya bukaci kakakin na kwamitin kamfen din Tinubu, ya rika mutunta mukaminsa na SAN ya dena yin karya kawai don yana son tallata Tinubu.