Gwamnatin jihar Kano ta ce za’a dawo da ƙarɓar Harajin kullum-kullum na matuƙa Baburan Adaidai Sahu a faɗin jihar nan
Kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano Engr. Muhammad Diggol ne ya bayyana haka a yammacin jiya Juma’a a helkwatartar Hukumar KAROTA
Lokacin da yake ganawa da Ƙungiyoyin sufurin Adaidai Sahu na jihar nan, ya ce ya zama wajibi Gwamnatin ta ci gaba da karbar harajin ga matuƙa Adaidai Sahu domin ciyar da jihar Kano ta ɓangaren sufuri gaba
Kwamishinan ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za’a sabunta rijistar Adaidaita Sahu domin tantance matuƙan, tare da sanin adadinsu a faɗin jihar Kano
Yace za’a ɓullo da sabbin tsare-tsare waɗanda za su sauƙaƙawa matuƙan biyan harajin kullum-kullum tare da sabunta rijistar ba tare da an musguna musu ba, duba da yanayin da ake ci na matsayin rayuwa
Ya ce ya zama wajibi Gwamnati ta san mutanen da suke tuƙa Adaidai Sahun duba da yanayin da ake ciki. A don haka ko wanne matuƙi dole ne sai ya samu shaidar sa hannu daga Mai Unguwarsa kafin a yi masa rijistar, hakan zai taimaka wajen inganta tsaro a fadin jihar nan baki daya
A nasa jawabin Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir yace sun kula da yadda siyasa ta lalata ɓangaren sufuri a fadin jihar nan, a don haka ba za su zuba ido su bar ɓarakae ta ci gaba da faɗaɗa ba, dole ne a dauki matakin ɗinkin ɓarakar
Ya ja hankalin ƙungiyoyin Adaidai Sahun su haɗa kansu su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya domin cin gajiyar tsare-tsaren da gwamnati ke shirin bijiro da shi da manufufinta na ciyar da jihar Kano ta ɓangaren sufuri gaba
Taron ya samu halartar Kwamishinan ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano Engr. Muhammad Diggol da shugaban Hukumar KAROTA Engr Faisal Mahmud Kabir da mai bawa Gwamna Shawara a ɓangaren sufuri na jihar Kano Maisalati Garko da kuma kungiyoyin Adaidai Sahu baki ɗaya
Signed
Nabilusi Abubakar
K/Nai’sa
Public Relations Officer
KAROTA
09/09/2023