‘Yan bindiga a Najeriya sun kwashe akalla mutane 50 da suka halarci bikin aure a Sokoto lokacin da suke komawa Gusau ta Jihar Zamfara a karshen makon nan.
Shaidun gani da ido sun ce da yammacin jiya ne ‘Yan bindigar suka tare hanyar lokacin da masu bikin ke komawa gida, inda suka bude wuta akan daya daga cikin motocin dake cikin tawagar su abinda ya tilasta musu tsayawa.
Rahotanni sun ce tawagar masu bikin ta fito ne daga Tambuwal lokacin da take komawa birnin Gusau, kuma nan take Yan bindigar suka kwashe matafiyan suka gudu da su cikin daji.
‘Yankin arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da fuskantar hare haren ‘Yan bindiga wadanda ke kashe matafiya da mazauna karkara tare da garkuwa da wasu domin karbar diyya.