Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PRP Kola Abiola, ya bayyana cewa za a kawo karshen yajin aikin da ke gudana na malaman ASUU watanni biyu kafin babban zaben 2023.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kola ya magantu ne a wajen binne marigayi dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP a jihar Ogun, David Bamgbos, ya ce yana takarar shugaban kasa ne don dakile tsarin rashin taimakon yan kasa.
A cewar sa gwamnatin tarayya za ta magance rikicinta da malaman ASUU ne watanni biyu kafin zabe
Ya kara da cewa gwamnati za ta kawo karshen yajin aikin ne don dalibai da dama su samu damar yin zabe saboda zai zamana sun yi rijista ne a gida.
Dan takarar wanda ke rike da tutar Peoples Redemption Party ya kuma bayyana cewa yana nan a cikin tsaren shugaban kasa na 2023 don lashe zabe