Joe Biden ya Isa fadar king Charles ll

Shugaba Biden ya isa London jana’izar gawar sarauniya.
Walid Y Hari

A daren jiya, Shugaban Amurka Joe Biden da mai ɗakinsa Jill Biden sun isa Birtaniya inda suka sauka a filin jirgin Standsed.

Jami’an Birtaniya ne suka karɓi baƙoncinsu tun daga filin jirgin inda suka tafi zuwa birnin London.

Shugaba Biden na daga cikin shugabannin duniya 500 da manyan baƙi da aka gayyata zuwa London jana’izar Sarauniya Elizabeth.

Kwambar motoci masu yawa, ciki har da motar shugaban mai sulke da ake kira “The Beast”, suka bar filin jirgin Stansted tun kafin 12:00 na dare.

Ana sa ran Mista Biden da sauran manyan baƙi za su yi bankwana da gawar Sarauniya a inda aka ajiye gawar, wato Westminster Hall kafin a binne ta a gobe Litinin.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments