Daga khadija Salisu Danmaliki
ABIN BUKATA
Da farko za’a tanadi wake gwargwadon bukata
Sai Indomie ita ma haka amma za’a auna duk ledar indomie 1 wake gwangwaje 1
Sai a tanadi Maggi
Gishiri Cokali
Curry tea Spoon
Mangyada Babban Ludayin Miya 1
Albasa Babba
Attarugu
Tattasai Manya
Timatir Manya
Nama Ko Kifi duk wanda ya samu.
Yadda ake HADAWA
Zamu dafa nama ya dahu mu zuba masa dan gishiri da Albasa, sai mu sauke. sannan musa mai awuta mu soya nama da kayan miya sai mu zuba ruwa rabin kwanonsha.sannan musa su maggi curry da gishiri sannan mu bar ruwan ya tafasa, sannan mu dauko wake da muka dafa, amma anaso yafi na wanda za’a hada da taliya dahuwa sai a juye a tafasashshen sanwar sai akawo Indomie A ɓallata biyu azuba, sannan A juya ahankali, sai asa yankakken Albasa, sai a rufe idan ya nuna Asauke SHIKENAN