Lamarin ya faru ne a birnin Ikko, kamar yadda rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Lagos ta tabbatar.
Tun da fari wadanda ake zargin sun bi farar safiya Ne wajan yin kutse tare da kai farmaki a sashin tsaro na bankin kuma suka Sami nasarar balle maballin tsaron wani Asusu inda suka tura Naira Miliyon N523,337,100, zuwa Asusu 18 a cikin Bankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda sashin yaki da damarar yanar gizo SP Eyitayo Johnson, yace kudin daga Asusu 18 an raba su zuwa wasu Asusu 225.
Ya kara da cewa a yanzu haka an Sami nasarar tare wasu kudaden da suka kai Naira N160,287,071.47 kuma daya daga cikin masu Asusu da aka rarraba kudaden yazo hanu.