Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Sameul Aruwan, ya bayyana cewa, sojojin Najeriya sun yi nsararar halaka wani dan bindiga da ya yi kaurin suna, da wasu ’yan bindiga da ke addabar al’umma a fadin kananan hukumomi uku na jihar Kaduna a wani harin da sojoji suka kai ta sama a ranar Litinin din da ta gabata.
Kwamishinan ya shaidawa manema labarai a Kaduna cewa, an kai farmakin ta sama kan ’yan bindigar ne a kananan hukumomin Birnin Gwari da Igabi da kuma Chikun da ke Kaduna, inda suka far wa sansanonin ’yan bindigar tare da lalata su.
Aruwan ya bayyana shugaban ’yan fashin da aka kashe, a harin da aka kai da jirgin da sunan “Alhaji Lawan”, inda ya ce an kuma ruguza sansaninsa.