Masana kimiyya sun ce akwai yiwuwar a ci nasara wajen tabbatar da wata ƙwayar hana haihuwa, bayan gano wani sinadari da ke iya hana maniyyi tafiya zuwa wurin da ƙwayaye suke.
Ƙwayar ana iya amfani da ita ne a lokacin da namiji zai kusanci mace.
Gwajin da aka yi a kan ɓeraye ya nuna cewa ƙwayar ta hana maniyyi tafiya na ƴan sa’o’i, ta yadda ba zai iya kai wa wurin ƙwayaye ba.
Ana buƙatar ƙara yin wasu gwaje-gwajen, inda za a yi a kan zomaye kafin a kai ga ɗan’adam.
Idan aka yi nasara, hakan na nufin mai son amfani da ƙwayar zai sha ta ne kimanin awa ɗaya kafin saduwa, sannan ya lura da tsawon lokacin da ƙwayar za ta daina aiki.
Yaya ƙwayar take aiki?
Ba kamar ƙwayoyin hana haihuwa na mata ba, wannan ƙwayar ba ta tasiri kan sanadarai masu tafiyar da lamurran jikin ɗan’adam (hormones).
Masana kimiyya sun ce wannan wani alfanu ne da suke son cin gajiyarsa – kasancewar ba za su kawo nakasu a kan sanadarin mazantaka na testosterone ba.
A gwaji na farko-farko da aka yi kan ɓeraye, wanda Kwalejojin Harkokin Lafiya na Amurka suka ɗauki nauyin gudanarwa, ya nuna cewa shan ƙwayar guda ɗaya da aka yi wa laƙabi da TDI-11861, na hana maniyyin namiji tafiya gabanin saduwa, ko a lokacin saduwar, ko ma bayanta.
Ƙwayar ta yi aiki na tsawon kusan awa uku. Amma an gane cewa ƙwayar ta daina aiki gaba ɗaya bayan awa 24 da shan ta. Inda maniyyi ya ci gaba da tafiya kamar yadda ya saba.
Ɗaya daga cikin masu binciken, Dr Melanie Balbach ya ce akwai alamun haske wurin tabbatar da nasarar ƙwayar wadda za a iya amfani da ita cikin sauƙi.
Idan har ta tabbata cewa tana aiki a jikin bil’adama, hakan na nufin maza za su iya amfani da ita a lokacin da suke da buƙata kawai.
“Kuma maza za su iya amfani da ita wajen yanke hukunci kan ko suna son su haihu, domin akwai” in ji Dr Balbach.
Sai dai ƙwayar ba za ta kare mutum daga cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar mu’amala tsakanin mace da namiji ba.
Farfesa Allan Pacey na jami’ar Sheffield ya ce “akwai buƙata sosai ta neman samar da ingantacciyar ƙwayar maganin hana haihuwa ga maza, wadda za ta iya aiki na ƙaramin lokaci, to amma duk ƙoƙarin da aka yi a baya bai kai ga nasara ba.”
“Wannan tsari na kashe sinadaran da ke taimaka wa maniyyi wajen tafiya sabon tsari ne fil, wanda ba a taɓa yi ba a baya. Kuma yana da ƙayatarwa musamman ganin cewa za a iya amfani da shi na lokaci ƙanƙani.