Yau da safe an kirawo ni na je gidan wani Alhaji domin na duba wata jaririya da aka haifa a gidansa sati uku da suka huce.
Da na je gidan an yi min korafin (complain) cewa yarinyar kamar sun fuskanchi ba ta gani tin bacin ranar da aka yi sunanta har izuwa yanzu da nake sanar da ku wannan labarin.
Domin iyayenta sun fuskanci jaririyar ba ta kula haske (response to light) ko kuma motsin hannaye a wajen fuskarta ko idanunta.
Wannan ya sa na ce bari na kirawo musu wani likitan yara a asibitin Nassarawa, kuma na kira na yi masa bayani. Sai ya ce wannan sai dai su je wajen likitan ido.
Abin mamakin da ya sa nake gaya muku wannan bayani shine: Da na kirawo likitan idanu sai ya ce an yi taran suna a gidan ko? Sai na ce masa an yi sosai ma.
Sai ya ce yanzu an gano cewa da yawa yaran da aka yi taron suna a gida kuma ‘yan uwan miji da mata suka dinga anfani da wayarsu wajen yiwa jariri ko jaririya hoto yana kashe idon jariri bacin haihuwarsa da wata daya ko biyu.
Abinda ya ke faruwa shi ne hasken flash daga kamerar waya yana shiga cikin idanun yaro a lokacin da ‘yan uwansa suke san sai yaran ya bude ido sannan za su daukeshi a hoto.
To a wannan lokacin wannan flashlight din ya ke lalata wani sashe na halittar idon mai suna retina a turance dake kai sako cikin kwakwalwar yaro domin fahintar abinda yake kallo.
Yi wa jariri hotuna a lokacin suna ya kan iya jawowa jariri makanta ta har abada.
Dan Allah sai mu dinga kula. Kuma mu sanar da iyaye da ‘yan uwa akan ilar wai sai dolle jariri ya bude ido anyi masa hoto.
Abubakar I Ahmad… SNAnephrology