Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Legas ta cafke wata mata mai shekaru 26 mai suna Maria Ahmadu da wata matar yar kimanin shekaru 25, mai suna Oge Okolie, a lokacin da suke ƙoƙarin siyar da jaririn da maria ta haifa ɗan watanni biyu a kan kuɗi Naira 300,000.
An bayyana cewa asirin su ya tonu ne bayan kammala ciki da Okolie ta ɗauki jaririn da zimmar ta kai wa wanda ya siya, a dai-dai lokacin ne jami’an tsaro suka yi nasarar damƙeta bayan ta shiga wata mota ƙirar bus a unguwar Oshodi da ke Legas.
Mahaiyar mai suna Maria ta ce mijinta bai damu da kula jaririn ba sannan kuma ta na so ta magance wasu matsaloli na gida da suka addabeta
Yan sandan sun kuma yi nasarar damƙe wacce ta shiga tsakani wajen gudanar da cinikin jaririn
Buƙatar kuɗi ce ta sanya ta yunkurin aikata hakan kuma jaridar Daily Trust, tace ‘yan sandan sun bayyana cewa ba su samu nasarar damƙe mai siyan jaririn ba, saboda ya riga da ya cika wandonsa da iska.
An bayyana cewa asirin su ya tonu ne bayan da Okolie ta ɗauki jaririn da zimmar ta kai wa mai siye, wanda a lokacin ne jami’an suka yi nasarar damƙeta bayan ta shiga wata mota ƙirar bus a unguwar Oshodi da ke Legas.
Da take bayar da bayani a hannun hukuma, mahaifiyar jaririn ta bayyana cewa tana cikin tsananin buƙatar kuɗi domin ta magance wata matsala ta gida.
A cewar mahaifiyar jaririn ta yanke shawarar siyar da shi ne tunda mahaifinsa bai damu da kula da shi ba.
“Ina buƙatar kuɗin ne domin in warware matsala a cikin gida tun da mahaifin jaririn bai nuna ya damu da kula da yaron ba.”