Wasu fasinjojin motoci guda biyu kimanin su 10 sun rasa rayukan su sanadiyar wani mummunan hadari da ta faru a jihar Oyo
Mota mai kirar Mazda da wata mai kirar hayis masu lambobi LEM 963 XA and NSR 222 ZS sune suka yi tawo mu gama
Shugaban Hukumar kula da afuwar hadura ta kasa reshen jihar Oyo, Joshua Adekanye, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace motar daya ta taso ne daga birnin Ikko daya kuma daga jihar Nasarawa.
Yace lamarin ya faru ne daga tazarar kilomita 12 a Ijawaya kan titin Oyo zuwa Ogbomoso da misalin karfe biyar da rabi na yamma
Kana rahoton ya tabbatar da mutuwar mutane 10 ta hanyar konewa kurmus
Daga karshe shugaban hukumar ta road safety na jihar Oyon ya ja hankalin direbobi da su kauracewa Dabiar nan ta gudun wuce sa a da kuma yin lodi fiye da kima.