Wata mata mai ɗauke da Juna biyu ta shiga ban ɗaki domin tattaunawa da kawarta a waya kan yaudarar maza da cin amanarsu.
Da take ba ƙawarta labarin cewa baki ɗaya maza makaryata ne, matar ta kira Mijinta ‘Sheɗan’ amma batasan yana laɓe yana ji ba.
A kalaman da ta yi da kawarta ta wayar salula, matar tace ba ta cire wa kowa hula ba baki ɗaya maza makaryata ne har da Mijinta Sai dai Matar mai juna biyu bata san cewa Mai gidanta na jin duk abinda take faɗa a waya ba cikin mamaki da kaɗuwa .
Daɗin daɗawa matar ta misalta Mai gidanta da, “Sheɗan” yayin da take ba da labarin yadda take sa masa ido a ko da yaushe .