Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sun kama mota dankare da kayan abinci da za a kaiwa ‘yan bindigan dake da maboya a Dangulbi a karamar hukumar Maru ta jihar, jaridar Premium Times ta rahoto.
Zamfara: ‘Yan sanda Sun Kama Mota Dankare da Kayan Abinci da Miyagun Kwayoyi Za a Kaiwa ‘Yan Bindiga.
A takarda da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu yasawa hannu a ranar Laraba, ‘tace yan sandan sun damke mutum takwas dake kai wa ‘yan bindiga bayanai, harsasai carbi 250 na AK47 da shanun sata 47.