Turkiyya ta sami karuwar masu yawon bude Ido

Yawan masu yawon bude ido daga kasashen waje da suka ziyarci Istanbul a shekarar 2022 ya karu da kashi 77 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata inda ya kai miliyan 16 da dubu 18 da 726.

Bisa kididdigar da Hukumar Al’adu Da Yawon Bude Ido ta Lardin ta fitar, yawan masu yawon bude ido daga kasashen waje da suka ziyarci birnin ya kai miliyan 16 da dubu 18 da 726 a shekarar 2022.

Adadin masu yawon bude ido da suka ziyarci birnin, wanda ya kai mutane miliyan 9 da dubu 25 da 4 a shekarar da ta gabata, ya karu da mutane miliyan 6 da dubu 993 da 722 a shekarar 2022.

A Istanbul, wanda Jamusawa suka fi ziyarta a shekarar da ta gabata, ‘yan Rasha ne suka kasance a matsayi na farko a shekarar 2022.

A bara, ‘yan Rasha miliyan 1 da dubu 495 da 24 sun ziyarci birnin.

Kasar Rasha ta kasance mai masu yawon bude ido miliyan 1 da dubu 237 da 314, Jamus mai masu yawon bude ido miliyan 1 da dubu 97 da 993, Amurka mai masu yawon bude ido dubu 717 da 107, Ingila mai masu yawon bude ido dubu 613 da 199, Faransa mai masu yawon bude ido dubu 567 da 475, Isra’ila mai masu yawon bude ido dubu 473 da 563, Iraki da dubu 423 da 945, Saudiyya mai yawan masu yawon bude ido dubu 390 da 353 sai Kuwait mai yawan masu yawon bude ido dubu 388 da 926.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments