Rahotanni na nuni da cewa nan da wata mai zuwa kasarsar kamaru za ta fara zagaye na biyar na alluran riga kafin annobar cutar COVID-19 a fadin kasar.
Minsitan kiwon lafiya na kasar Manaouda Malachie, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka raba manema labarai.
Yace za a fara aikin riga kafin ne daga ranar 18 zuwa 27 ga watan Nuwamba, kuma za a yi wa mutane masu shekaru 18 zuwa sama, da wadanda suka riga suka karbi riga kafin, da mata masu juna biyu da ma masu shayarwa.
A cewar ministan, a wani bangare na riga kafin yaki da COVID-19, ya zuwa wannan lokaci kasar Kamaru ta yi wa kashi 12 cikin 100 na al’ummarta masu shekaru 18 zuwa sama alluran riga kafin sama da miliyan 1.8.
Ya bayyana cewa, wadannan sakamako masu karfafa gwiwa da aka samu, ba su isa su kare kasar daga wani sabon barkewar cutar ba. Ya kara da cewa, duk da lafawar annobar da aka samu a cikin ‘yan watannin nan, har yanzu ana samun wadanda ke kamuwa da cutar. Kuma burin kamfel din riga kafin a fadin kasar, shi ne samun garkuwar jiki baki daya a fadin kasar