Jiya ne, aka kammala taron yini biyu na ministocin harkokin wajen kasashen G20 a New Delhi, babban birnin kasar Indiya.
Taron ya fitar da takaitaccen bayani da takardun sakamakon shugaban, inda ya yi kira da a kara karfafa hadin gwiwar bangarori daban-daban don tinkarar kalubalen duniya baki daya.
Takardar ta jaddada cewa, a halin yanzu duniya tana fuskantar kalubale masu tarin yawa, wadanda suka hada da tafiyar hawainiya wajen cimma muradun ci gaba mai dorewa na MDD, da matsalar sauyin yanayi, gurbatar daji, da koma bayan tattalin arziki, da matsaloli na bashi, rashin farfadowa bayan annobar COVID-19, karuwar talauci da rashin daidaito, barazanar karancin abinci da makamashi, lalacewar tsarin samar da kayayyaki na duk duniya, da karuwar tashe-tashen hankula da rikice-rikice tsakinin shiyya-shiyya..
Indiya ce mai rike shugabancin karba-karba na G20 na bana. A jawabin da ya gabatar da kafar bidiyo a jiyan, firaministan Indiya Narendra Damodardas Modi ya bayyana cewa, duniya na fatan G20 za ta dauki matakan da suka dace kan kalubalen ci gaban da ake fuskanta, da jurewar tattalin arziki, da daidaito na harkoki kudi, da samar da abinci da makamashi, da saukaka yanayin siyasa da matsin da ake ciki a wasu yankuna.