Real Madrid za ta biya Yuro miliyan 1 ga Lyon saboda wani katabus a kwantiragin Karim Benzema, bayan da dan wasan ya lashe kyautar Ballon d’Or ta bana a yammacin ranar Litinin.
Bafaranshen ya koma Los Blancos daga Lyon a shekara ta 2009.
Benzema ya ci wa Madrid kwallaye 328, wanda shi ne na biyu mafi girma a tarihin kulob din, bayan tsohon abokin wasansa Cristiano Ronaldo.
Dan wasan mai shekaru 34, ya zura kwallaye 44 a raga a gasar La Liga da kofin zakarun Turai.
Wata magana da kungiyoyin suka amince a lokacin da Benzema ya koma babban birnin Spain daga Lyon a shekara ta 2009 yana nufin cewa Real Madrid za ta biya €1m (£870k) ga kulob din Ligue 1, saboda abin da ya hada da lashe kyautar Ballon d ’Or.
“Yaro ne da muka ga ya girma kuma muka ga ya bunkasa. Mun gan shi ya yi nasara a kusan duk abin da ya yi, “Shugaban Lyon, Jean-Michel Aulas, ya ce bayan bikin.