Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanar da wani sabon shiri na inganta rayuwar al’ummar jihar da ke Arewa maso Yamma, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
A wani abin da ya kira da bunkasa tattalin arziki da rage zaman kashe wando, Gwamna Namadi, ya kaddamar da wani shiri na samar da attajirai 150 a wa’adinsa na farko a ofis.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a wurin raba tallafin dogaro da kai ga mata 1,000 wanda ma’aikatar kula da harkokin mata ta jihar Jigawa ta shirya da haɗin guiwar hukumar matasa.
Da yake jawabi a wurin taron ranar Alhamis, gwamna Namadi ya ce:
“Wannan rana ce mai muhimmanci gare mu a jihar Jigawa yayin da muka kudiri aniyar kawo sauyi da ci gaba ga al’umma. Gwamnatinmu na gano basirar jama’ar ta kuma mun shirya buɗe musu hanyoyin samun arziƙi.”
“Akwai babban wannan da zai zo nan gaba, kuma da yardar Allah daga nan zuwa shekaru hudu masu zuwa, za mu tabbatar da samar da mutane 150 masu dogaro da kai da za a kira masu kudi a jihar nan.”
Daga ƙarshe, Gwamnan ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar shirin ba da tallafin da su yi amfani da abinda suka samu ta hanyar da ta dace kana su gina wa kansu gobe mai kyau.