Jam’iyyun adawa ne ke taɗile ƙoƙarin Buhari na magance rikicin kuɗi — Lai Mohamed
Gwamnatin Tarayya ta zargi wasu jam’iyyun adawa da taɗile ƙoƙarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na samar wa ƴan Najeriya sauki game da radadin rashin kuɗaɗe sakamakon sake fasalin Naira.
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya yi wannan zargi a taron nuna ƙwazon mulkin shugaban Buhari daga 2015 zuwa 2023, karo na 23 a yau Talata a Abuja.
An shirya shirin ne domin nuna irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu.
Taron na yau ya karɓi bakuncin Ministar Agaji, Magance Ibtila’i da Ci gaban Jama’a, Sadiya Umar-Farouk.
A jawabinsa na bude taron, Mohammed ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi la’akari da irin matsalolin da ƴan kasa ke fuskanta sakamakon sake fasalin kudin Naira da kuma matsalar man fetur.
Ya ce gwamnati na aiki tukuru don magance matsalolin tattalin arzikin guda biyu, inda ya ƙara da cewa kuma za a dauki karin matakai don rage radadin ga ƴan Najeriya.
Ministan ya tuna cewa bayan ganawarsa da gwamnonin jam’iyyar sa ta APC, shugaban kasar ya bukaci ƴan Najeriya da su ba shi kwanaki bakwai don warware matsalolin da ke tattare da aiwatar da sabon tsarin na Naira.