Hadin guiwar jami’an ‘yan sanda na kasashe 11 sun murkushe manhajar damfara ta FluBot wadda ta karade sassan duniya, yayin da wasu miyagu ke amfani da ita wajen satar bayanan sirrin jama’a.
Kwararrun ‘yan damfara na amfani da wannan manhaja ta FluBot wajen yi wa jama’a leken asiri a cikin wayoyinsu na zamani, inda suke kwashe bayanan sirrikansu domin sace hatta kudaden bankunan jama’ar.
Jami’an ‘yan sandan Netherlands sun ce, sun yi nasarar katse dubun-dubatan wannan manhaja ta FluBot daga wayoyin mutane, yayin da suka kare wasu karin mutane miliyan 6 da dubu 500 daga fadawa cikin tarkon ‘yan damfarar.
Hukumar ‘Yan Sandan Kasashen Turai ta Europol ta ce, manhajar FluBot na cikin miyagun manhajojin damfara da ke yaduwa a kasashen duniya cikin sauri kuma tamkar wutar daji.
Yanzu haka ‘yan sandan na ci gaba da farautar ‘yan damfarar da suka kirkiri tare da baza shu’umar manhajar cikin wayoyin jama’a.
Kasashen da a halin yanzu suka zurfafa bincike kan manhajar sun hada da Australia da Amurka da Belgium da Finland da Hungary da Ireland da Romania da Spain da Sweden da Switzerland da kuma Netherlands.