Manchester United na shirin gabatar wa Tottenham tayin fam miliyan 80 a kan dan wasanta na gaba dan Ingila Harry Kane, bayan da babban jami’in kungiyar ta Old Trafford Richard Arnold ya amince a yi cinikin.(Star)
Bayern Munich na son sayen dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Mason Mount.(Times)
Manchester United ba ta yi wani yunkuri na yarda da wata sabuwar yarjejeniya tsakaninta da Marcus Rashford ba. (Athletic)
Har yanzu Chelsea ba ta fara wata sabuwar tattaunawa kan kwantiragin dan wasanta na tsakiya ba Mateo Kovacic, wanda kuma Manchester City ke sha’awa. Dan wasan na Crotia yana da sauran wata 16 da suka rage masa yanzu a kungiyar. (Standard)
shirye Liverpool take ta biya sama da fam miliyan 60 domin sayen dan bayan Napoli da Koriya ta Kudu Kim Min-jae, mai shekara 26, wanda Manchester United ma ke so. (Rai)
Arsenal na sha’awar sayen dan wasan tsakiya na Denmark Jesper Lindstrom, mai shekara 23, wanda Eintracht Frankfurt za ta saki a kan kusan yuro miliyan 30. (Sport 1)
Namibia ta ci Kamaru ta koma ta daya a kan teburi
Har yanzu Manchester City na jiran dan wasan tsakiya na Jamus Ilkay Gundogan ya yanke shawara kan makomarsa, amma kuma Barcelona na matukar son daukar dan wasan mai shekara 32 a kyauta idan bai sabunta zamansa a City ba. (Fabrizio Romano)
Idan har Gundogan ya tafi, City za ta nemi sayen matashin dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund da Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, da kuma matashin dan tsakiya na Bayer Leverkusen da Jamus Florian Wirtz, shi ma mai shekara 19 domin maye gurbin. (Football Insider)
Duk kungiyar da ke son kociyan Brighton Roberto de Zerbi to dole sai ta cake mata kudi lakadan, kuma sai a bazara ta gaba za a yi cinikin dan Italiyar ba a wannan kakar ba. (Fabrizio Romano)
A halin da ake ciki kuma De Zerbi yana son samun karin iko a kan ‘yan wasan da kungiyar za ta saya ko ta sayar. (Mail)
Chelsea za ta sanya dan wasanta na tsakiya dan Ingila Ruben Loftus-Cheek a kasuwa a karshen kaka. (Football Insider)
Kungiyoyin Premier da dama ciki har da Leicester da Fulham da kuma Wolves, na sa ido a kan matashin dan wasan tsakiya na Lorient Enzo le Fee na Faransa bayan da ya tabbatar yana son barin kungiyar ta Faransa a bazaran nan. (90 min)
Tottenham ta tabbatar da cewa ta cimma yarjejeniyar kafin kwantiragi ta daukar matashin dan wasan gaba Herbie James, mai shekara 16 dan Ingila tsawon shekara uku daga cibiyar renon matasan ‘yan wasa ta Manchester City. (Football London