Daga Sadik Lamin Hassan
Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga Hukumar Kula da Jami’oi ta kasar da sauran masu ruwa da tsaki, da su dakatar da duk wasu lamuransu har sai bayan kammala zaɓe.
Ta kuma yi kira ga Hukumar Zaɓe INEC ta samar da wani tsari na musamman ga ɗalibai domin su karɓi katinsu na zaɓe.
Wannan ya biyo bayan ƙudurin da Ɗan Majalisar Kabiru Ibrahim Tukura ya gabatar na mukatar gaggawa ga mutane, a yayin tattaunawar kwamitinsu.
Da yake gabatar da wannan ƙuduri, yace tsarin karatun makarantun gaba da jami’a ya ci karo da tsarin zaɓe, mafi yawan ɗalibai ba za su samu damar yin zaɓen ba, makarantu ba su duba ranar zaɓe ba.