An bukaci gwamnatin tarayya da ta jihohi da kananan hukumomi da su samar da tsarin da zai magance kauar da maaikatan lafiya suke yi zuwa kasashen ketare
Bukatar hakan ta fito ne ta bakin mataimakin Daraktan yakin neman zaben Gawuna Garo, Dakota Umar Tanko Yakasai yayin gabata da bitar yini guda da kungiyar sa mai suna Grass Root Movement for Asiwaju Bola Ahmed Tunubu shettima and Gawuna Garo ta shirya wanda ya gudana a Avenue events center.
Yayin taron Dakta Umar Tanko Yakasai yace shi da tsohon kwamishinan lafiya na jihar Lagos da tsohuwar kwamishinar lafiya ta jihar Borno sunga dacewar shirya taron wayar da kan Daliban lafiyar ne kasancewar sune maaikatan lafiyar kasar nan a nan gaba.
Tun da fari Dalibai da suka fito daga jami’o’i daban-daban a jawaban su da dama sun nuna sha’awar su ta fita kasashen ketare domin gudanar da aiki a can da zarar sun Sami damar hakan
Wasu daga cikin Dalibai da suka nuna sha’awar su ta fita kasashen ketaren sun hada da
Sulaiman Yahaya shugaban kungiyar Dalibai masu koyon aikin jinyar ta kasa reshen B U K
Da kuma Jibril Aliyu Shehu shugaban kungiyar Daliban likitanci ta kasa reshen B U K wanda ya Sami wakilcin Muhammad Murtala Abdullahi
Ita kuwa a nata jawabin Dacta Zainab Datti Admed ta ja hankalin Dalibai masu burin tafiya kasashen ketare da su tsaya suyi karatun ta nutsu a cewar ta aiki a kasashen waje ba abune mai dadi ba
Tace tayi aiki a ketare taji irin wahalar da ake sha ta rashin cikakken yanci da rashin yin uzuri a lokutan aiki.
A cewar ta a kasashen waje zaka yi musu aiki ne tamkar inji kuma babu wata yabawa daga wandanda suka baka aikin.
Daga karshe Dacta Yakasai ya bayyana cewa taron sun gudanar da makamancin sa a babban birnin tarayya Abuja da Lagos da kuma nan Kano kuma zasu tattara raayiyyikan Dalibai da suka samu za su mika su ga Dantakarar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu da Dantakarar gwamnan Kano Dacta Nasiru Yusuf Gawuna domin magance lamarin.
Taron ya sami halartar manya mutane a fannin lafiya David suka hada da kwamishinan lafiya na jihar Kano da sauran maaikatan lafiya daga bangarori daban-daban.