Atletico Madrid na son sayen dan wasan Manchester City dan kasar Jamus, Ilkay Gundogan, mai shekara 32. wanda ya lashe Premier League hudu da kwantiraginsa zai kare a karshen kaka mai zuwa a Etihad, Bayern Munich ma na son daukar dan wasan. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Dan wasan Napoli dan kasar Georgia, Khvicha Kvaratskhelia, wanda Liverpool da Chelsea ke so dauka, farashinsa zai kai £86m. Mai shekara 21 ya bayar da gudunmuwar da kungiyarsa ta samu gurbin kai wa zagaye na biyu a Champions League a bana. (London Evening Standard)
Manchester United ta lissafa dan kwallon Ingila, Jude Bellingham a matakin na sawun gaba da take son saya, bayan da Erik ten Hag ke shirin biyan £100m kudin cinikin dan kwallon mai shekara 19 daga Borussia Dortmund. (Daily Mirror)
United na mutukar son daukar dan wasan Bayern Munich dan kasar Kamaru, Eric Maxim Choupo-Moting, mai shekara 33. (Media Foot – in French)
To sai dai United ba za ra sayi dan wasa ba a watan Janairu, bayan da ta fitar da £225.4m kudin da ta sayo ‘yan kwallo biyar a bana. (Manchester Evening News)
Manchester United na shirin daga darajar yarjejeniya da Diogo Dalot don kada dan wasan mai shekara 23 ya bar kungiyar haka arha a karshen kaka mai zuwa, bayan da Barcelona da AC Milan ke bibiyar Dalot. (Sun)
Dan kwallon Chelsea, Jorginho, mai shekara 30, na fatan ci gaba da taka leda a kungiyar, duk da cewar Barcelona na son daukar dan wasan. Kwantiragin tsohon dan wasan Napoli zai karkare a karshen kaka mai zuwa. (Fabrizio Romano on Twitter)
Ana cewa Totenham na shirin sayen dan wasan Chelsea dan kasar Morocco, Hakim Ziyech, mai shekara 29, wanda karawa daya ya yi a Premier League a kakar nan. (Express)
An bai wa Arsenal damar daukar dan kwallon Benfica, mai tsaron bayan tawagar Sifaniya, Alejandro Grimaldo, mai shekara 27 a kaka mai zuwa. (CaughtOffside on Twitter)
Dan kwallon tawagar Brazil mai taka leda a Arsenal, Gabriel Martinelli, mai shekara 21, ya ce yana daf da tsawaita yarjejeniyarsa da Gunners mai jan ragamar Premier League, wanda ya zura kwallo biyar a raga a wasa 12 a kakar nan. (Mirror)
Lionel Messi baya son barin Paris St-Germain ba tare da lashe babban kofi ba, saboda haka kyaftin din Argentina na tattaunawa kan tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar. (L’Equipe – in French)
West Ham da Nottingham Forest da Leeds na son daukar dan kwallon tawagar Senegal mai shekara 25, Boulaye Dia, wanda ke buga wasannin aro a kungiyar Salernitana ta Serie A daga Villarreal ta Sifaniya. (Gazzetta dello Sport – in Italian, subscription required)