Daga Sadik Lamin Hassan
A ranar 1 ga watan Nuwamba ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso zai ƙaddamar da kundin manufofin mulkinsa idan ya ci zaɓen shugaban kasa.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘dage bikin kaddamar da kundin manufofin shugaban kasa da kuma taron RMK na 3,’ wanda jam’iyyar NNPP ta fitar a yau Talata.
Jam’iyyar ta kuma sanar da ɗage taron lakcoci na RMK na 3, inda ta ce a yanzu za a gudanar da taron ne a ranar 31 ga watan Oktoba.
Ya ce dage zaben ya biyo bayan bukatu da ‘ya’yanmu suka yi a fadin kasar, da kuma bayan tuntubar juna da masu ruwa da tsaki.
A wani bangare sanarwar ta kara da cewa, “Taron makalolin da za’a gudanar karo na 3 na RMK wanda wani ɓangare ne na gudanar da bikin cikar Mai Girma Tsohon Gwamna, Engr Sen Dr Rabi’u Musa Kwankwaso shekaru 66 da haihuwa, yanzu zai gudana ne a ranar Litinin 31 ga Oktoba 2022 da karfe 10:00 na safe a A. -Class Park and Events Center, Wuse II, Abuja.
“A wannan rana, Mai Girma tsohon gwamna zai gana da Shuwagabannin Jihohi, Yan takarar gwamnoni da ‘Yan Takarar Sanata da sauran masu ruwa da tsaki domin yin nazari tare da duba tsarin sa ga Nijeriya da ƴan Nijeriya, yayin da kaddamar da tsarin zai zo a ranar Talata 1 ga watan Nuwamba. 2022.