An shiga zaman dar-dar bayan da gobara ta tashi a ofishin hukumar shirya jarrabawa Afirka ta Yamma, WAEC, da ke Yaba, Jihar Legas, rahoton The Punch.
Ana juyayin akwai mutane da dama a cikin ginin a yayin da wutar ke cigaba da bazuwa.
Gobara Ta Tashi A Ofishin WEAC, Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Makale A Ciki.
A halin yanzu ba a san sanadin tashin wutar ba. Amma, ma’aikatan bada agajin gaggawa sun isa wurin an kuma kashe gobarar.
Majiyoyi sun bayyana cewa karuwar wutar lantarki a wani ofishin hukumar ne ya janyo gobarar. Da farko an fara ganin hayaki a saman ginin a yayin da wutan ke kona wasu ofisoshi.