Babban kotun tarayya dake zaune a birnin tarayya ta ɗage sauraron ƙarar da wasu gwamnoni suka shigar suna ƙalubalantar wa’adin Babban Bankin Najeriya na amfani da tsofaffin kuɗi.
Alƙalin kotun John Okoro, da ke sauraron karar ya bayyana ranar uku ga watan Maris a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraron ƙarar bayan ji daga lauyoyin dukkanin ɓangarorin biyu.
Tun da fari gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 31 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 1,000, da 500, da kuma 200.
Sai dai daga baya shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da ƙara wa’adin zuwa 10 ga watan Fabarairu.
Amma duk da haka gwamnonin jihohin Kaduna da Zamfara da Kogi suka shigar da ƙarar a ranar uku ga watan Fabarairu suna ƙalubalantar wa’adin na gwamnatin tarayya.
Sannan a lokacin zaman kotun na ranar 15 ga watan Fabarairu, wasu gwamnonin jihohi bakwai suka mara musu baya wajen ƙalubalantar matakin na gwamnatin tarayya.
Kazalika a ranar takwas ga watan Fabarairu kotun ta dakatar da gwamnatin tarayya daga aiwatar da wa’adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin.
Sai dai daga bisani gwamnan babban bankin tarayya na CBN ya bayyana cewa matakin sa na daina amfani da tsofaffin takardun 1000 da 500