Wata babbar Kotu a jahar Kano ta zartar da hukuncin Kisa ta hanyar rataya ga wadansu mutane hudu, da suka aikata laifin fashi da makami, tare da hallaka Alhaji Isyaku Muhammad, mai Gida lamba 6, layin Masana, kusa da Unguwar Hotoro dake jahar.
By Kabir Abdullahi Dukawa
Kotun Karkashin jagorancin mai shari’a Nasiru Saminu ta tabbatar da cewa, wadanda ake zargin sun aikata laifin ne bayan gabatar mata da kwararan hujjoji da Barista Ahmad Wada da ma’aikatar shari’a ta jahar Kano suka yi a gaban ta.
Wandanda Kotun ta zartarwa da hukuncin sun hada da Rotimi Abe da Musa Babbatunde ( Danyarbawa ) da Kabiru Sule da kuma Sunday Ofokwu.
Bayan karanta musu tuhumar da ake yi musu, Maryam Isyaku Muhammad ta gabatar da shaidu guda Uku, a gaban Kotun inda shaida ta farko tace, a ranar 22, ga watan Janairu, shekara ta 2002, tana kwance da daddare a dakin ta da Kanin ta, Yan fashin suka karya kofar dakin suka shiga suka tashe ta harda yi mata barazanar Fyade.
A yayin da ta kara gabatar wa da Kotu shaida ta biyu da na Uku daga cikin yayan marigayin sun tabbatar wa da Kotun cewa, su Sunday Ofokwu da abokan sa guda sun shiga gidan su da daddare da bindiga da wasu muggan makamai inda suka razana su, bayan sun kama addu’a cikin razani suka umarci babar su ta basu Kudi, indai suna bukatar tsira da rayuwar su.
Matar mamacin tunda fari ta shaida wa Kotu cewa, a ranar 17, ga watan Afurilu shekara 2002, suna zaune a gida suna Kallon labaran Talabijin na Kasa ( Network News ) sai taga an hasko su Sunday Ofokwu a Helkwatar rundunar yan Sanda ta Kasa a Abuja, anyi holan su bisa wani aikin ta’addanci da suka aikata a Harry Marshall.
Ta kara da cewa, nan da nan washe gari ta gaggauta sanar da rundunar yan Sanda ta jahar Kano cewa, sun gano mutanen da suka shiga gida suka aikata musu fashi da makami tare da kashe baban yaran ta, da kwace mu su Naira miliyan daya tare da Sarka na Gwalagwalai.
Da yake yanke hukunci mai shari’a Saminu yace duba laifin da suka aikata ya saba wa doka ta 97 da 298 da kuma 221, na dokokin hukunta laifuka na Kasa, inda a laifin farko fashi da makami, ya yanke musu hunkuncin Daurin rai da rai a gidan gyaran Hali.
Mai shari’a Saminu inda a laifi na biyu, aikata Kisan Kai, Sunday Ofokwu da abokan sa guda Uku, an yanke musu hukunci Kisa ta hanyar rataya.