Babban abokin hamayyar shugaban kasar Saliyo mai barin gado a zabe mai zuwa, ya kawar da wata babbar matsala da ka iya hana shi tsayawa takara.
Samura Kamara, wanda Julius Maada Bio ya doke shi a zaben 2018, yana fuskantar shari’a tun watan Fabrairu bisa zargin cin hanci da rashawa.
Magoya bayansa wadanda suka ce lamarin na da nasaba da siyasa, suna fargabar za a yanke masa hukuncin gaggawa wanda zai hana shi shiga zaben da za a yi ranar 24 ga watan Yuni.
Sai dai mai magana da yawun hukumar zaben ya ce, Kamara ya gabatar da bukatarsa na yin takara a hukumance a ranar Litinin, matakin da ya biyo bayan umarnin dage ci gaba da shari’ar tasa har zuwa ranar 14 ga watan Yuli.
A gefe guda kuma, wata babbar kotu a jiya Talata ta ba da umarnin a saki fasfo din Kamara, wanda zai ba shi damar halartar taron kungiyar Commonwealth a Biritaniya, kamar yadda kakakin sashin shari’a Elkass Sannoh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.