Kasar Sin wa to Chana ta kaddamar da wata manhaja ta butunbutumi da nufin aiki safarar wutar lantarki wanda mahukunta a kasar sukace hakan zai magance dauke wutar lantarki kwata-kwata a kasar ta China.
A rahoton da Murtala Zhang ya fitar yace Jiya Jumma’a ne aka kafa wani yanki na musamman a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin, inda aka shimfida layukan jigilar wutar lantarki masu tsawon kilomita 3.24, dan amfani da mutum-mutumin wato Robot da sauran wasu na’urori masu sarrafa kansu, don tabbatar da samar da wadatacciyar wutar lantarki ba tare da daukewa ko sau daya ba a kowace rana.
Kasancewar zaa Iya cewa wannan itace fasaha ta farko da da aka samar a wannan fanni Amma an ingantata so sai.