Gobe ne ranar Dimokradiyya ta 2023, ana sa ran Shugaba kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, 2023, da misalign karfe 7 na safe, Vanguard ta ruwaito.
Wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gidan gwamnati, Abiodun Oladunjoye ya fitar a ranar Lahadi, ta bukaci gidajen talabijin, rediyo, da sauran kafafen yada labarai da su hada kai don yada jawabin Tinubu.
Wannan shine karo na farko da shugaba Tinubu zai yiwa ‘yan Najeriya bayani a hukumance tun bayan hawansa mulki mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
An rantsar da Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu Idan baku manta ba, an rantsar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban kasan Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun da ta gabata.