Jiragen sama sun shiga yajin aiki a kasar France

Ma’aikatan jiragen sama a Faransa na shirin shiga yajin aiki domin neman karin albashi, matakin da zai tilasta soke tashin jirage da dama a yau  Alhamis.

Yajin aikin zai girgiza bangaren sufurin jiragen sama a Turai a daidai lokacin da kasashen nahiyar ke shan wahala wajen kula dimbin fasinjoji sakamakon karancin ma’aikata.

Tuni hukumomin kula da filin jiragen sama na Charles de Gaulle da ke birnin Paris na Faransa suka bukaci kamfanonin jiragen da su takaita adadin jiragen da za su yi balaguro a tsakanin karfe 7 na Safiya zuwa karfe 2 na rana daga gobe Alhamis.

Kamfanin Jirgin sama na Air France, ya ce, tuni ya soke tashin jirage har guda 85 da ke tafiyar dogo da garejen zango.

Kungiyoyin Ma’aikatan Filin Jiragen Saman sun bukaci mambobinsu da su yi fitar-dango domin neman a kara musu Euro 300 akan albashinsu ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Ma’aikatan sun ce, ba a yi musu adalci wajen biyan su hakkokinsu duk da cewa, kamfanonin jiragen na samun riba mai yawa a yanzu, baya ga dimbin fasinjojin da ke balaguro akai-akai.

Bangaren sufurin jiragen saman ya samu koma-baya shekaru biyu da suka gabata sakamakon barkewar annobar Covid-19, lamarin da ya sa aka sallami da dama daga cikin ma’aikata.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments