Rahotanni na nuni da cewa wasu fusatattun yan daba Daga hauren Manlesi sun kai harin ramuwar gayya a unguwar Yakasai Kofar Nasarawa da misalin karfe tara na daren Jiya Litinin biyo bayan rauni da yakai ga cire hanun Dan uwan su da akayi a lokacin zaben fidda gwani da ya gabata kimanin makonni biyu da suka wuce.
Daga Abdulhamid Isah D Z
Shedan gani da ido da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaidawa wakilin Aksammedia Abdulhamid Isah D Z cewa wasu yan hauren suka shiga unguwar ta Yakasai suka haun mutane da sara tare da kwace musu wayoyi.
Yace babu wanda ya sami mummunan rauni kasancewar an kira jamian sintiri kuma sun halarci filin da ake Fadan a lokacin da ya dace.
Bayan shawo kan rigimar ne D Z ya ji ta bakin kwamandan vigilantee na unguwar Dirimin zungura, Kwamanda Mahir, inda yace sun sami kira ne daga Al’ummar unguwar Yakasai Kofar Nasarawa cewa wasu bata Gari suna fada tare da kwace wayoyi mutane, kuma a take suka kira gangamin jamiansu na Dirimin Zungura da bakin Asibiti da Yakasai da kuma na Kofar Nasarawa suka shiga wajan da abin ya shafa kuma cikin taimakon Allah suka shawo kan rikicin.
A karshen yace wadanda aka kama zasu mika su zuwa ofishin yan sanda domin gudanar da bincike kuma suna kyautata zaton da angama bincike za’a gurfanar da su a gaban Kotu domin su girbi abin da suka shuka.