Kungiyar matuka motocin Akorikura ta kasa reshen railway dake nan jihar kano,ta bayyana Dr. Mukhutar Danmajen kano a matsayin shugaban da yake fafutika domin ci gaban kungiyoyi da alummar Najeriya baki daya.
Shugaban kungiyar Alh. Abubakar Daniya Bala shine, ya bayyana haka a lokacin da kungiyar ta kai masa ziyara da kuma, jinjina masa saboda kokarin da yake yi domin ganin Alummar sun ci gaba ta fannoni da dama.
Abubakar Daniya,yace,irin wadannan sune mutanen daya kamata a sanya wajen jagorantar Alumma da shugabantarsu domin Nemo musu mafita ta yadda za su dogara da kawunansu da taimakawa wadanda suke a karkashinsu.
Shugaban ya jaddada cewa,kungiyar mutuka motacin Akorikura za ta ci gaba da baiwa jagororin da suke son ci gaban kungiyoyin da alumma cikakken goyan bayan da ya dace,musamman domin su ci gaba da tallafawa jama,ar jihar kano da ma kasa baki daya.
Haka zalika,shugaban kungiyar ya yayi fatan Allah yasa wannan sabuwar Gwamnatin da za ta karbi mulki,ta bijiro da managartan shirye shirye da za su taimaka wajen farfado da jihar kano da tattalin arzikinta musamman bangaren harkokin sufuri da kasuwanci da sauran fannin ayyuka.
Ya kuma, bukaci yankungiyar da su kasance masu bin dokokin da Gwamnati ta sanya da hukumomin kula da al,amuran sufuri da kasuwanci da kasancewar jihar kano ciyabiya ce,ta kasuwanci.
A jawabinsa Dr. Mukhutar Danmajen kano, ya sha alwashin ci gaba da tallafawa kungiyoyin dalibai da masu sana,oi Dana matasa da harkokin sufuri wajen ci gaban alummar Najeriya baki daya.
Dr.mukhutar ya shawarci kungiyoyi masu zaman Kansu da su kara jajircewa wajen bijiro da tsarin da zai taimakawa alummar jihar kano da ma kasa baki daya, inda yace,yanzu lokaci ya sauya dole ne sai alumma sun hada Kansu wajen kawo sauyi tsakanin jama,a Wanda hakan yana kawo ci gaban alummar da kasa baki daya.
Daga nan yayi fatan Allah ya kara habaka tattalin arzikin jihar kano da samun zaman lafiya mai dorewa hadin kan alumma da bunkasa harkokin matasa da kiwan lafiya.
Ibrahim sani gama pyramid radio.