An kaddamar da hari a kan babban ofishin hukumar zaben Najeriya INEC a Owerri babban birnin jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.
An kai harin ne da safiyar yau litinin inda rahotanni suka ce ‘yan bindiga fiye da 10 suka diranma ofishin.
Wata majiya ta bayyana cewa ofisoshi uku ne suka kama da wuta kafin jami’an tsaro su kai daukin gaggawa inda suka kashe mahara uku.
Kakakin ‘yan sanda a jihar Imo, CSP Mike Abattam ya tabbatar da kai harin amma bai yi wani karin bayani ba.
“Da safiyar yau litinin ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Ipob ne sun kai hari a ofishin Inec inda suka wurga bam din da ake hadawa da fetur,” in ji Abattam.
A cikin ‘yan watannin nan ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar aware ta IPOB ne suna yawan kai hare-hare a ofisoshin INEC da ke kudu maso gabashin Najeriya.