An bukaci Al’ummar Arewa da su jajirce wajan wayar da kan al’umma kan suje su bude Asusu a bankuna domin a tafi dasu a kowanna yanayi na ci gaba idan yazo.
Bukatar hakan ta fito ne ta bakin Mahmood Abdullahi malami a kwalejin tarayya ta jihar Kano wato FCE Kano a zantawar sa da Wakilin Aksammedia Abdulhamid Isa Durumin zungura.
Da yake tsokaci game da takaita adadin kudin da za’a dauka a bankuna a kowanne sati 100,000 ga kowanna mutum da kuma 500,000 ga kamfanoni yace abune mai kyau kuma ci gaba ne da zai haifar da da mai Ido.
Yace kimanin kaso 90% cikin 100 na yan Najeriya basa amfani da Naira 100,000 a sati guda kuma duk abin da aka ce kaso 10 cikin 100 ya shafa babu dalilin da zai sa a rika caccakar sa.
Ya kara da cewa ba cece-kuce ne ya dace da mutane ba face su rungumi wayar da kan al’umma amfanin takaita yawan kudade a hannayen su
A ranar Asabar din da ta gabata gwamnan babban banki a zantawar sa da manema labarai yace lamarin takaita daukar kudi ba’a yi shi on musgunawa kowa ba face kawo ci gaba ga kasa.