Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ta yi la’akari da shawarar da kwamatin ƙarbar mulki ya bayar kan batun kadarori mallakin gwamnatin jihar da gwamnatin da ta shude ta cefanar.
Abba ya ce saboda haka ya sanar da cewa, daga wannan rana duk wasu filayen jama’a da kadarorin da gwamnatin Ganduje ta wawashe tare da siyar da su jami’an tsaro su karɓe su har sai lokacin da gwamnati za ta yanke hukunci a kansu
“Mun lura cewa gwamnatin da ta shuɗe ta sayar da filaye a makarantu, Gidajen tarihi, masallatai, asibitoci, maƙabartu da wuraren hutawar jama’a, da kuma gefen ganuwar birnin Kano” in ji shi
Ya ce gwamnatin baya ta kuma sayar da kadarorin gwamnatin jihar Kano masu yawa a ciki da wajen jihar ga ƴan uwansu da ƴaƴansu ba ba bisa ƙa’ida ba.