Majalisar zartarwa ta jihar kano ta Kara kudaden gudanarwa ga masarutun Jihar Kano guda 5 domin cigaba da aikin da suka saba gudanarwa.
Sanarwar na kunshe ne cikin jawabin da Kwamishinan yada labarai na Jihar kwamared Muhammad Garbage, a yau alhamis 15-09-2022..
Muhammad Garba, yace duba da yawan al’umma da sauran nauye nauyen dake Kan majalisar masarautar Kano gwamnatin ta rubanya alawus din masarautar daga miliyan hamsin zuwa miliyan dari.
” Su Kuma sauran Masarautun guda hudu wadanda suka haɗa da Bichi, Rano Karaye da Gaya an Kara musu daga Naira Miliyan 20 ya koma Naira Miliyan 40 domin inganta aiyukan su”. Inji kwamishinan
Ban janye daga takarar majalisar tarayyar Gezawa da Gabasawa ba – ‘Yar takarar PDP
Ya kara da cewa majalisar ta amince da fitar da naira miliyan dari Uku da hudu domin biyan alawus na malamai dari biyu da tamanin da bakwai na jami’ar Yusuf maitama sule.