Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ware kudi naira biliyan 1.2 don aikin hanyoyi 42 a cikin birnin Kano
Kwamishinan yada Labarai na jihar Kano Muhamud Garba shine ya bayyana hakan ga manema labarai, ya ce tuni aka kafa kwamitin da zai yi nazari kan lamarin harma an zabi wasu kamfanoni da za su yi aikin.
Malam Muhammad Garba ya nanata kudirin gwamnatin Ganduje na samar da ababen more rayuwa don kyautata rayuwar al’ummar jihar.
Ya ce za a kashe kudaden ne kan aikin gina shataletale, gyara da kuma kula da hanyoyin da ke bukatar gyara sakamakon ambaliyar ruwa da rarake su.
Kwamishinan ya ce wasu daga cikin shataletalen da ake shirin gyarawa akwai na gidan mai na A A Rano da First Bank, da sauransu
Ya kuma bayyana cewa an kafa kwamiti da suka hada da injiniyoyi na ma’aikatar ayyuka, hukumar tsare-tsare da ci gaba na jihar da kuma sauran ma’aikatu, da hukumomi don su yi nazari kan lamarin don daukar matakin gaggawa.
kwamishinan ya kuma ce tuni kwamitin ya tuntubi kamfanonin kwangila wanda an zabi wasu don aiwatar da ayyukan.